Posts

Shari'ar Musulunci Zata Yi Aiki A Masana'ar Tace Fina-finai Ta Jihar Kano

Image
  Hukumar Tsaftace Fina-Finai Ta Jihar Kano Zata Haɗa Guiwa Da Ma'aikar Addinin Jihar Domin Sanya Ƙafar Wado Ɗaya Ga Masu Karan Tsaye Da Dokokin Hukumar. Sakataren zartarwa na Hukumar Tace Fina-finai na Jihar Kano, Abba El-mustapha ya jaddada aniyarsa ta yin aiki kafada da kafada da ma’aikatar shari’a domin inganta ci gaban hukumar. El-mustapha ya bayyana haka ne ga babban mai shari’a kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano Alh Haruna Isah Dederi a jiya yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai ma’aikatar

Tsugunni fa bata ƙare ba a Nijar

Image
A sanyin safiyar ranar Lahadi dubun-dubatan al'ummar Nijar ne suka fito zanga-zanga a kofar dandalin Toumo dake birnin Yamai, domin nuna goyon bayansu ga juyin mulkin da sojojin kasar suka yi wanda ya hambarar da shugaba Bazun. Ga wasu hotonan masu zanga zanagar. Bashar Muhammad.

Sabuwar ShopRite da aka Buɗe a Kaduna

Image
 'Yan Jihar Kaduna sun samu hadaddiyar Shoprite. Ku kalli Hoton yadda take 

Rundunar Yan Sandar Jihar Kano Ta Bada Umurnin Kama Masu Tunzura AA Rufa'i

Image
Rundunar yan sandar jihar kano ta ba da umurnin faɗaɗa bincike tare da gayyato waɗan da ake zargi da amfani da sunan AA Rufa'i wajen tunzura shi. Kwamishinan yan sandar jihar kano CP Mohammed Usaini Gumel ya bada umurnin ta bakin mai magana da yawun rundunar Asp Abdullahi Haruna Kiyawa a lokacin da wasu Lauyoyi suka shigar da ƙorafi akan masu amfani da rashin lafiyar matashin da akewa laƙabi da Alhaji AA Rufa'i. Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne iyalan AA Rufa'i suka yi hannunka mai sanda ga masu amfani da sunan domin samun suna a kafafen sadarwa, Inda suka ce za su ɗauki matakin Shari'a ga duk wanda aka samu da laifin hakan ko waye shi. Bashar Muhammad. 26/07/2023

Ma'aikatan Jihar Ogun Za Su Sami Tallafin 10,000 Daga Gwamnatin Jihar.

Image
Gwamnatin Jihar Ogun dake kudancin Nigeria ta amince da bayar da tallafin kuɗi Naira dubu 10, 000 ga ma'aikata da kuma masu karbar fansho a jihar. Kamar yadda al'ammura suke faruwa a kasa da kuma yanayin kunci da wahala da al'ummar jihar suke ciki, gwamnatin Jihar Ogun a kokarin ta na rage raɗaɗi da wahalhalun da cire tallafin man fetur ya haifar ta ce zata bayar da tallafin tsabar ƙudi Naira 10,000 ga kowani ma'aikacin gwamnati ciki kuwa har da masu karbar fansho. Baya ga wannan gwamnatin Jihar ta amince da matakai kamar haka; Bayar da alawus-alawus na haɗarin gaggawa ga duk ma'aikatan lafiya da likitoci a jihar. Bayar da alawus-alawus na musamman ga ma'aikatan gwamnati a jihar. Gaggauta bayar da takardun ƙarin aiki na Shekar 2021 da na 2022. Sauran sun haɗa da taimakon tsabar ƙudi na gaggawa dun biyan garatuti ga masu karbar fansho.  Mayan ma'aikata da manyan hukumomi su tabbatar sun tsara hanyoyin da ma'aikatan dake ƙarƙashinsu ba sa aiki kullum domin...

ZAMU ƊAUKI MATAKI AKAN MASU ƊAUKAR HOTO KO BIDIYON RUFA'I

Image
Za mu ɗauki matakin Shari'a ga duk masu ɗaukar Rufa'i wurare daban-daban suna masa hoto da bidiyo cewar; danginsa A daai-dai lokacin da hotona da bidiyon Rufa'i Wanda wasu suke wa laƙabi da Hamshaƙin mai kuɗin duniya "bilget" suka karkaɓe shafukan sada zumunta, iyalansa sun koka akan yadda mutane ke amfani da rashin lafiyarsa domin neman suna a shafukansu na sada zumunta. Iyalan sun ce hakan bai dace ba kuma za su ɗauki matakin ba sani ba sabo ga duk waɗan da suka ci gaba da yin haka. Ko a jiya bayan wasu bayin Allah sun kai shi asibiti, likitoci sun tabbatar cewa tsokanar da ake yiwa Lawan Rufai (Alhaji Rufa’i) na kara masa rashin lafiya Haryanzu dai gwamnati bata ce komi ba akan batun Rufa'i, amma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama ta human rights Watch ta shiga lamarin. Yanzu dai iyalan Rufa'i sun tabbatar da cewa duk wanda ya kara tsokana ko tunzura wannan bawan Allah, za su dauki matakin shariah a kan sa ko waye. Shin baya ga haka ko akwai wani mata...

ZAMBA TA YANAR GIZO.

Image
Kotu ta yanke wa wasu dalibai 5 hukuncin daurin shekaru biyu biyu a gidan yari bisa samun su da laifin zamba ta yanar gizo. Mai shari’a Darius khobo na babbar kotun jihar Kaduna ne ya yanke wa daliban biyar; chidebre Stanley Opera, wanda ke da'awar; Avail Hollywood, Manasseh Sefa Ephraim, wanda aka fi sani da Felicia dannyels, Victor Odeh wanda aka fi sani da Christopher Anderson, Chukwukere Obinna Paul wanda aka fi sani da "Shaun Lee" da kuma Enyogu Etim Ekpo wanda aka fi sani da "Henry Wilson" hukuncin bayan da aka tuhume su laifukan zamba daban-daban da suka shafi intanet. Rundunar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC yankin shiyar Kaduna ce ta kama wadanda ake tuhumar a samame daban-daban da hukumar ta gudanar a kaduna. Waɗan da ake tuhumar sun kasance suna haɗa kai domin kwamusa tare da ƙirƙirar shafukan sada zumunta na zamani na bugi dun damfarar waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, galibi baƙaƙen fata. An dai zarge Chidebre...