ZAMBA TA YANAR GIZO.

Kotu ta yanke wa wasu dalibai 5 hukuncin daurin shekaru biyu biyu a gidan yari bisa samun su da laifin zamba ta yanar gizo.





Mai shari’a Darius khobo na babbar kotun jihar Kaduna ne ya yanke wa daliban biyar; chidebre Stanley Opera, wanda ke da'awar; Avail Hollywood, Manasseh Sefa Ephraim, wanda aka fi sani da Felicia dannyels, Victor Odeh wanda aka fi sani da Christopher Anderson, Chukwukere Obinna Paul wanda aka fi sani da "Shaun Lee" da kuma Enyogu Etim Ekpo wanda aka fi sani da "Henry Wilson"  hukuncin bayan da aka tuhume su laifukan zamba daban-daban da suka shafi intanet.

Rundunar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC yankin shiyar Kaduna ce ta kama wadanda ake tuhumar a samame daban-daban da hukumar ta gudanar a kaduna.
Waɗan da ake tuhumar sun kasance suna haɗa kai domin kwamusa tare da ƙirƙirar shafukan sada zumunta na zamani na bugi dun damfarar waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, galibi baƙaƙen fata.

An dai zarge Chidebre Stanley Opera cewa a watan Mayu, 2023 ya kwaikwayi wani Ba'amurke mai suna Avail Hollywood a manhajar aika saƙo ta "Google chat" abin da ya saɓawa sashe na 308 na dokar Penal code ta Jihar Kaduna.
Hakazalika, ana zargin Victor Oche Odeh da aikata laifuka da suka haɗa da zamba ta hanyar yaudara da karya da kuma basaja ga wani bature Christopher Anderson daga watan Janairu zuwa Yulin wanann shekara da muke ciki,  

Wadan da ake tuhumar dai sun amince sun aikata laifukan da ake tuhumarsu akai.

A dun haka Mai shari’a Khobo, a ranar 22 ga watan Yuli, 2023 ya yanke wa wadanda ake tuhumar hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari ko kuma biyan tarar N150,000 kowanne.

Hakazalika, za su hannunta duk wani abu da suka samu ta wanann hanya ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Bashar Muhammad.

Comments