ZAMU ƊAUKI MATAKI AKAN MASU ƊAUKAR HOTO KO BIDIYON RUFA'I
Za mu ɗauki matakin Shari'a ga duk masu ɗaukar Rufa'i wurare daban-daban suna masa hoto da bidiyo cewar; danginsa
A daai-dai lokacin da hotona da bidiyon Rufa'i Wanda wasu suke wa laƙabi da Hamshaƙin mai kuɗin duniya "bilget" suka karkaɓe shafukan sada zumunta, iyalansa sun koka akan yadda mutane ke amfani da rashin lafiyarsa domin neman suna a shafukansu na sada zumunta.
Iyalan sun ce hakan bai dace ba kuma za su ɗauki matakin ba sani ba sabo ga duk waɗan da suka ci gaba da yin haka.
Ko a jiya bayan wasu bayin Allah sun kai shi asibiti, likitoci sun tabbatar cewa tsokanar da ake yiwa Lawan Rufai (Alhaji Rufa’i) na kara masa rashin lafiya
Haryanzu dai gwamnati bata ce komi ba akan batun Rufa'i, amma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama ta human rights Watch ta shiga lamarin.
Yanzu dai iyalan Rufa'i sun tabbatar da cewa duk wanda ya kara tsokana ko tunzura wannan bawan Allah, za su dauki matakin shariah a kan sa ko waye.
Shin baya ga haka ko akwai wani mataki da kuke ganin ya dace iyalansa su ɗauka?
Muna dakon amsa a comment section.
Bashar Muhammad.

Comments
Post a Comment