Rundunar Yan Sandar Jihar Kano Ta Bada Umurnin Kama Masu Tunzura AA Rufa'i
Rundunar yan sandar jihar kano ta ba da umurnin faɗaɗa bincike tare da gayyato waɗan da ake zargi da amfani da sunan AA Rufa'i wajen tunzura shi.
Kwamishinan yan sandar jihar kano CP Mohammed Usaini Gumel ya bada umurnin ta bakin mai magana da yawun rundunar Asp Abdullahi Haruna Kiyawa a lokacin da wasu Lauyoyi suka shigar da ƙorafi akan masu amfani da rashin lafiyar matashin da akewa laƙabi da Alhaji AA Rufa'i.
Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne iyalan AA Rufa'i suka yi hannunka mai sanda ga masu amfani da sunan domin samun suna a kafafen sadarwa, Inda suka ce za su ɗauki matakin Shari'a ga duk wanda aka samu da laifin hakan ko waye shi.
Bashar Muhammad.
26/07/2023

Comments
Post a Comment