Ma'aikatan Jihar Ogun Za Su Sami Tallafin 10,000 Daga Gwamnatin Jihar.

Gwamnatin Jihar Ogun dake kudancin Nigeria ta amince da bayar da tallafin kuɗi Naira dubu 10, 000 ga ma'aikata da kuma masu karbar fansho a jihar.




Kamar yadda al'ammura suke faruwa a kasa da kuma yanayin kunci da wahala da al'ummar jihar suke ciki, gwamnatin Jihar Ogun a kokarin ta na rage raɗaɗi da wahalhalun da cire tallafin man fetur ya haifar ta ce zata bayar da tallafin tsabar ƙudi Naira 10,000 ga kowani ma'aikacin gwamnati ciki kuwa har da masu karbar fansho.

Baya ga wannan gwamnatin Jihar ta amince da matakai kamar haka;

Bayar da alawus-alawus na haɗarin gaggawa ga duk ma'aikatan lafiya da likitoci a jihar.

Bayar da alawus-alawus na musamman ga ma'aikatan gwamnati a jihar.

Gaggauta bayar da takardun ƙarin aiki na Shekar 2021 da na 2022.

Sauran sun haɗa da taimakon tsabar ƙudi na gaggawa dun biyan garatuti ga masu karbar fansho. 

Mayan ma'aikata da manyan hukumomi su tabbatar sun tsara hanyoyin da ma'aikatan dake ƙarƙashinsu ba sa aiki kullum domin rage musu tasirin Karin farashin man fetur a tsakaninsun da akalla kashi 20 cikin 100.

Raba kayan abinci irinsu shinkafa, gari, wake, masara da sauransu ga masu rauni a jihar.

Har ila yau, za a samar da takin zamani da sauran kayan amfanin gona ga manoma a kan farashi mai sauƙi, da dai sauran matakai na rage raɗaɗi akan cire tallafin man fetur.


Bashar Muhammad.

Comments

Popular posts from this blog

ZAMBA TA YANAR GIZO.