Kotu ta yanke wa wasu dalibai 5 hukuncin daurin shekaru biyu biyu a gidan yari bisa samun su da laifin zamba ta yanar gizo. Mai shari’a Darius khobo na babbar kotun jihar Kaduna ne ya yanke wa daliban biyar; chidebre Stanley Opera, wanda ke da'awar; Avail Hollywood, Manasseh Sefa Ephraim, wanda aka fi sani da Felicia dannyels, Victor Odeh wanda aka fi sani da Christopher Anderson, Chukwukere Obinna Paul wanda aka fi sani da "Shaun Lee" da kuma Enyogu Etim Ekpo wanda aka fi sani da "Henry Wilson" hukuncin bayan da aka tuhume su laifukan zamba daban-daban da suka shafi intanet. Rundunar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC yankin shiyar Kaduna ce ta kama wadanda ake tuhumar a samame daban-daban da hukumar ta gudanar a kaduna. Waɗan da ake tuhumar sun kasance suna haɗa kai domin kwamusa tare da ƙirƙirar shafukan sada zumunta na zamani na bugi dun damfarar waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, galibi baƙaƙen fata. An dai zarge Chidebre...