HARI A GIDAN ATIKU
ABUBUWAN DA YA KAMATA KU SANI GAMI DA HARIN DA AKA KAI GIDAN DAN TAKAR SHUGABAN KASA A JAM'IYYAR PDP, ALHAJI ATIKU ABUBAKAR
A ranar Talata 25/07/2023 rundunar ƴan-sanan jihar Adamawa ta sanar da kama mutum hudu (4) da ta ce sun amsa cewa su ƴan-Boko Haram ne, bayan sun yi yunƙurin kai hari a gidan tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan-takarar shugaban ƙasa na jamiyyar PDP a zaɓen da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar.
To amma akwai ɗaure kai sosai a wannan lamarin, musamman ganin cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake tsaka da shari'ar zaɓen 2023.
Wani babban abin gwara-kan ƴan-ƙasa a kan wannan lamari shi ne, ambatar sunan Boko Haram, ƙungiyar da a can baya gwamnati ta yi ta iƙirarin cewa ta kawar da ita daga Nigeria. Kuma za a iya tabbatar da hakan sakamakon yadda aka kwashe dogon lokaci ba tare da an ji ɗuriyarta ba.
Abin lura a nan shi ne, Idan har Boko Haram —har kawo wannan lokacin— na da zarrar kitsa kai hari a wurare irin birnin Yola kuma a ƙofar gidan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, hakan na nufin kenan iƙirarin da gwamnatin APC ta tsohon shugaban kasa Buhari ta yi na kai ƙarshen Boko Haram, ƙarya ce!
Idan kuma kai ƙarshen Boko Haram ƙarya ce, kenan Gwamnatin Bola Tinubu na da jan aiki a gabanta, kamar haka:
1. Bincikar duk manyan hasfan sojojin da su ka yi yaƙi da Boko Haram tun zamanin Goodluck Jonathan zuwa yanzu.
2. Gurfanar da duk wanda aka tabbatar da hannunsa wajan yin saku-saku da baiwa Boko Haram damar yunƙurin tasowa tun daga Dajin Sambisa zuwa Yola domin ƙaddamar da mummunan hari. Ana ƙasa da mako guda da babban kwamandan operation Hadin-Kai ya ajiye aikinsa tare da hannunta ragwamar hukumar ga wani sabon hannu.
3. Karɓo maƙudan kuɗin da tsohon shugaban kasa Major General Muhammadu Buhari mai ritaya ya kashe wajan sayen makamai da kawar da Boko Haram daga arewa maso gabas.
Lalle ana wasa da hankalin ƴan Nigeria, kuma shugabanni su sani, duk sanda ƙura ta kai bango ƴan-ƙasa su ka shirya yin bore, za a sha mamaki.
Badamasi Bello Dinawa
25/07/2023

Comments
Post a Comment