Yaƙi da Juyin Mulki ko Yaƙi da Yan'ta'adda?
Yayin da wa'adin mako ɗaya da ƙungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Nijar su mayar da mulki ga hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum ya cika a ranar Lahadi, tana kasa tana dabo saboda duka ɓangarorin biyu na tsaka mai wuya wajen ɗaukar mataki na gaba kan wannan dambarwa.
Shi dai shugaban ƙungiyar ECOWAS kana shugaban Nigeria Alhaji Bola Ahmad Tinubu ya na fuskantar matsin lamba ga majalisar kasar inda ta nuna rashin goyon bayanta da bukatar sa na tura dakaron soja a Nigar.
Tuni dai shugaban ƙungiyar kuma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaƙabawa sojojin jerin takunkumai, kuma aka yanke masu wutar lantarki da suke samu daga Najeriya, da rufe masu iyakoki wanda hakan ke nufin ba abin da za a shigar a ƙasar, haka su ma ba za su fitar ba.
A bangare guda kuma, A Nigeria musamman jihohin arewa maso yamma da suka haɗa da Katsina, Zamfara, Sokoto da sauransu suke fama da matsanancin rashin tsaro, musamman wani rahoto dake nuna cewa ƙananan hukumomin Sokoto ta gabas da suka haɗa da Gada, sabon birni, gwaranyo suna fama da yaƙi da yan'ta'adda da suka hana su shakat.
Yanzu haka dai wasu rahotanni na nuna cewa abin sai dai Allah ya kyauta.
Shin mi yaka mata hukumomin Nigeria su yi, tura sojoji yaki Nijar ko yaki da 'yan ta adda a Nigeria?
Bashar Muhammad.



Comments
Post a Comment