Matashiya Yar'shekaru 28 Ta Zama Minista a Nijar.
Gwamnatin soji a Nijar sun Naɗa matashiya mai suna Guichen Aghaichata ATTA, Yar'shekaru 28, a matsayin sabuwar ministar yawon bude ido da kasuwanci ta kasar.
Wannan naɗi na zuwa ne bayan hambarar da shugaba Bazun a watan jiya.
Haryanzu ƙungiyar ECOWAS na adawa da juyin mulki da sojojin kasar Nijar suka yi.
Ita dai matashiya Aghaichata mace ce mai himma sosai wajen inganta dabi'un, al'adu da kuma kokari don kawo cigaba ga matasa.
Ta yi karatu idan da ta yi da digiri biyu a fannin kasuwanci a kasar Maroko.
Bashar Muhammad.

Comments
Post a Comment